Rikici ya lafa a Beirut | Labarai | DW | 26.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici ya lafa a Beirut

Jamian sojin kasar Libanon sun dake dokar hana fita da suka sanya a titunan birmnin Beirut ,sakamakon arangama da tsakanain magoya bayan gwamnati da masu adawa da ita ,wanda ya haddasa mutuwan mutane 4 ayayinda wasu 150 suka jikkata.Sai dai har yanzu jamioi da makarantu zasu cigaba da kasancewa a rufe,bisa ga umurnin gwamnati.Wannan rikici dai haila yau ya hadar fadan fito na fito da bindigogi tsakanin yan darikar sunni da shiawa.A jiya nedai aka gudanar da taron gidauniyar tallafawa ginin kasar ta Libanon a birnin paris din kasar faransa,inda kasashe sukayi alkawuran bada Euro Billion 6,domin tallafawa gwamnatin prime minista Fouad Siniora.