Rikici ya kabre tsakanin Fatah da Hamas a zirin Gaza | Labarai | DW | 15.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici ya kabre tsakanin Fatah da Hamas a zirin Gaza

Ƙungiyoyin Fatah da na Hamas na ci gaba da gwabza faɗa a zirin Gaza.

Daga ranar juma´a zuwa yau, mutane 17 su ka rasa rayuka a cikin ba ta kashin, wanda shine mafi muni, tun bayan girka gwamnatin haɗin kan ƙasa a watan Maris da ya wuce.

Wanda su ka rasa rayukan sun haɗa da sojoji 8 masu tsaran lahiyar shugaban hukumar Palestinawa, Mahamud Abbas.

Praministan Palestinu Isma´il Haniey, ya bayyana aika runduna ta mussamman, domin kawo ƙarshen wannan faɗace-faɗace,.

A cikin wannan mummunan hali ne, na tashe-tashen hankulla, ministan cikin gida, Hani Al-Qawasmeh, yayi murabus daga muƙamin sa.

Sakataran harakokin wajen ƙungiyar gamaya turai, Havier Solana,ya yi kira ga gwamnatin haɗin kan ƙasar Palestinu, ta gaggauta ɗaukar matakan kawo ƙarshen wannan rikici.