1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya barke a Bayelsa dake kudancin Nigeria

November 6, 2006
https://p.dw.com/p/Bud7

Masu zanga zanga dauke da makamai sun mamaye harabar kamfanin mai na Agip mallakar kasar Italia a kudancin Nigeria,wanda ke zama na baya bayan rigingimu dake ritsawa da Nigeriar dake zama jagorar albarkatun man Petur a nahiyar Afrika.Masu boren sun mamaye harabar kamfanin man Agip dake Tebidaba,wanda ke jihar Bayelsa,wanda ya tilasta maaikatan rufewa,inji Joshua Benamesia,dake zama jamiin tsaron gwamnan jihar ta Bayelsa.Ya sanarwa wa manema labaru a fadar gwamnati dake birnin Yenagua cewa,masu boren kan nemi da a biya musu bukatunsu ne,sai dai a wannan karon basu fani,me suke nema ba.Amma wani jamii daga daya daga cikin kauyukan ,ya sanar dacewa,suna neman hakkokinsu ne adangane da gurbata musu yanayi da masanaantun man ke yi,tare da samarwa alummomin yankunan aikin yi.Rahotanni daga birnon a kasar Italian dai na nuni dacewa,akwai maaikata kimanin 48 da suka hadar da jamian tsaro,alokacin da masu boren suka afkawa cibiyar da hari.Adangane da matakan tsaro ne aka rufe cibiyar nan take.