Rikici ya ɓarke tsakani sojoji da makiyaya a Uganda | Labarai | DW | 31.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici ya ɓarke tsakani sojoji da makiyaya a Uganda

A ƙalla mutane 27, da su ka haɗa da sojoji 16, su ka rasa rayuka,a yankin arewa maso gabacin Uganda,a sakamakon hito-na hito, tsakanin sojojin gwamnati, da mayaƙan galgajiya makiyaya.

Rikicin ya faru, a lokacin da dakarun gwamnati, su kayi dura mikiya a yankin, da nufin ƙwace makamai, daga al´ummomin mazauna yankin, mafi yawan su makiyaya.

Rahotani sun nunar da cewa, dakarun gwamnati sun yi nasara ƙwace makama, saidai sun wuce gona da iri, ta hanyar aikata kissan gilla, ga mutanen da ba su san hawa ba, balle sauka.

Gwamnatin Uganda, na zargin makiyayan, da yin anfanin da makaman da su ka mallaka, domin ƙuntatawa sauran jama´ar da ke zaune tare da su.