Rikici ya ɓarke a Palestinu | Labarai | DW | 13.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici ya ɓarke a Palestinu

Tashe-tashen hankula na ci gaba da ƙamari a Palestinu, inda daren jiya, zuwa sahiyar yau, wasu magoya bayan Jam´iyar Fatah da Mahamud Abbas, su ka ƙone wata cibiyar Hamas a birnin Napluse.

Wannan ƙone ƙone, na matsayin maida martani, ga harin da yan Hamas su ka kaiwa wata cibiyar tsaro a birnin Rafah da ke ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar palestinawa.

Sannan yan ƙungiyar Al Aksa, masu goyan bayan Fatah, sun banka wuta, ga majalisar dokoki da fadar gwamnatin Parminista, Ismail Hanniey, da ke birnin Rammallah.

Tashe tashen hankulla sun yi ƙamari tsakanin ɓangarorin 2, tun bayan da Mahamud Abbas, ya sa hannu a kann dokar shirya zaɓen raba gardama, a watan juli mai kamawa, domin jin ra´ayin jama´a a game da hanyoyin warware rikici tsakanin Isra´ila da Palsetinu.