Rikici tsakanin Fatah da Hamas na barazanar zama wani yakin basasa
June 12, 2007Fada ya kazanta tsakanin kungiyoyin Falasdinawa da ba sa ga maciji da juna wato Fatah da Hamas a Zirin Gaza. Rahotanni sun ce an halaka mutane 20 a sabon fadan da ya barke da sanyin safiyar yau talata. An lalata gidan FM Falasdinawa Isma´il Haniya a wani hari da aka kai kan gidan a yau. Jim kadan bayan haka wasu ´yan bindigan kungiyar Hamas sun farma hedkwatar jami´an tsaron kungiyar Fatah a birnin Gaza, bayan wani gurnati da aka harba a kusa da ofishin shugaban Falasdinawa Mahumd Abbas. Shugaban na Falasdinawa yayi kira da a kwantar da hankula. Sannan a lokaci daya ya zargi Hamas da kokarin kwace mulki da karfin tuwo a Zirin Gaza. A kuma halin da ake ciki kakakin kungiyar Fatah ya ce a wani lokaci a yau kwamitin tsakiya na kungiyar zai yi wani taro don tataunawa ko zasu saura cikin gwamnatin hadin guiwa da suka kafa da Hamas a cikin watan maris a wani mataki na kawo karshen tashe tashen hankula na cikin gida.