1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici tsakanin Dakarun Gwamnati da Tamil Tigers.

May 13, 2009

Hare-hare akan asibitin arewacin Sri Lanka ya kashe fararen hula

https://p.dw.com/p/HpWS
Asibiti a Sri LankanHoto: AP

Dakarun gwamnatin Sri Lanka na cigaba da matsowa yankin mayakan tawayen Tamil Tigers dake Arewa maso gabashin kasar, wanda hakan ya daɗa tsananta hare-hare tsakanin ɓangarorin biyu, Sai dai kuma fararen hula kusan dubu 50 ne suka tsinci kansu cikin halin kakanikaya a wannan yankin.

Ɓangaren dakarun gwamnati dai na cigaba da parpaganda da ikirarin nasarori da suke samu na kusan murkushe mayakan Tamil Tigers. Rundunar sojin gwamnatin dai na cigaba da matsowa zuwa wannan yankin. Sai dai 'yan tawayen na zargin Dakarun gwamnati da amfani da manyan miyagun makamai akan fararen hula. Zargin da Kakakin ma'aikatar harkokin tsaron ƙasar Rambukwala ya karyata a taron manema labaru daya gudanar a birnin Colombo...

Soldaten vor Einnahme von LTTE Hochburg im Norden Sri Lankas
Faɗa a arewacin ColomboHoto: picture-alliance / dpa

Ya ce "Muna karyata waɗannan zarge zagen ,domin karyace kaɗai a bangaren 'yan tamil Tigers. Nasarar da muke samu ba wai muna karawa fararen hula nauyi ba ne, amma kokarimmu shine ganin cewar mun ceto su daka cikin halin kunci da suke ciki a wannan yankin"

Sakamakon ƙaruwan yawan fararen hula da ke cigaba da tagayyara da kuma wannan zargin juna da ɓangarorin biyu dake faɗa ke cigaba dayi, itama ƙungiyar 'yan Tamil ta kira taron manema labaru, a karkashin jagorancin wakilinta a majalisar kasar kuma shugabanta Sambanthan, bayan harin daya ritsa da wani babban asibitin dake yankin 'yan tawayen wanda kuma yayi sanadiyyar mutuwan fararen hula masu yawa...

Ya ce "Dakarun gwamnati na cigaba da amafani da manyan miyagun makamai duk da tabbacin da gwamnati ta yi nacewar, ba za ayi amfani da irin waɗannan makamai ba. Wanda hakan yasa ake cigaba da tagayyara"

Sri Lanka Kindersoldaten der Rebellenorganisation LTTE
Mayakan TawayeHoto: AP

Babu dai yadda za a tabbatar da wannan zargi da ɓangarorin biyu ke yiwa juna, kasancewar dakarun gwamnati sun hana manema labaru da kungiyoyin bada agaji daman damar zuwa filin daga domin ganewa idanunsu, kokuma dauko hotunan ainihin yadda lamura suke tafiya. Kazalika an haranta yin hira da 'yan kabilar Tamil ɗin dake gudun hijira kasancewar dukkannin suna karkashin yankin gwamnati.

Majalisar Ɗunkin Duniya dai ta kiyasta cewar rikicin yankin arewacin Sri lankan ya ritsa da akalla mutane dubu 50, wadanda a yanzu haka basu da mafita, ga karancin abinci da ruwan sha, baya ga rashin hanyar samun jinya daga raunuka da suka samu a lokutan hari.

Sarasi Wijeratne itace kakakin ƙungiyar bada agajin kasa da kasa ta Red Cross.....

Ta ce "Halinda ake ciki yanzu ya hana damar kwaso marasa lafiya dake zube, ballantana ayi maganar sauke kayyayakin abinci wa mazauna yanakin. Akwai marasa lafiya da dama wasu ma suna cikin hali matsananci na jinya,akwai waɗanda suka rasa wasu gaɓobinsu a sakamakon wannan faɗa".

Mawallafiya:Zainab Mohammed

Edita: Umaru Aliyu