Rikici kan yankin Bakassi | Labarai | DW | 22.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici kan yankin Bakassi

Najeriya ta aike da ƙarin soji izuwa yankin Bakassi dake iyakarta da ƙasar Kamaru.Kafafen yaɗa labarai sun rawaito shugaban sojin ruwa na Najeriya, Mr Ganiyu Adekeye na tabbatar da wannan labari. Hakan dai a cewar mahukuntan na Najeriya ya biyo bayan kisan sojin Kamaru 20 ne tare da jikkata wasu 10 a yankin na Bakassi. Ta´asar da wasu tsageru na Najeriya su ka aikata, a yanzu haka ta haifar da kace nace, a tsakanin ƙasashen biyu. Tuni dai Najeriya ta ƙaryata zargin cewa akwai hannunta a kisan sojin na Kamaru. A dai watan Agusta na shekara ta 2006 ne Majalisar Ɗinkin Duniya ta mika yankin na Bakassi mai arziƙin mai ga ƙasar ta Kamaru.