1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici kan makamashin nukiliya: Iran ta yi watsi da sabon tayin da Kungiyar EU ta yi mata

YAHAYA AHMEDAugust 8, 2005

Maikatar harkokin wajen Iran ta ba da sanarwar cewa, a ran litinin 8 ga watan Agusta ne za ta ci gaba da gudanad da ayyukan sarrafa sinadarin yurenium a masana'antarta ta makamshin nukiliya da ke birnin Isfahan. Wannan sanarwar dai ta janyo hauhawar tsamari tsakaninta da kasashen Birtaniya, da Faransa da Jamus, wadanda su ne a madadin Kungiyar Hadin Kan Turai ke shawarwari da birnin Teheran don cim ma wata madafa a kan wannan batun da aka dade ana korafi a kansa.

https://p.dw.com/p/Bvab
Ma'aiktar azurta sinadarin yureniyum (Uranium) da Iran ta gina a birnin Isfahan.
Ma'aiktar azurta sinadarin yureniyum (Uranium) da Iran ta gina a birnin Isfahan.Hoto: AP

Iran ta fito fili ta yi watsi da tayin da Kungiyar Hadin Kan Turai ta yi mata game da rikicin da ake yi kan batun kafofin makamashin nukiliyan da kasar ke mallaka. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Reza Asafi ne ya sake nanata matsayin da kasarsa ta dauka a kan wannan batun, a wani taron maneman labarai a ran lahadin da ta wuce a birnin Teheran. Kafin hakan ma, sai da ministan harkokin wajen Iran din, Kamal Charrazi, ya bayyana rashin amincewarsa da tayin na Kungiyar Hadin Kan Turai. A ran litinin ne dai Iran din ta ce za ta sanad da Kungiyar Hadin Kan Turan a rubuce game da matsayinta.

Batun da ake ta korafi a kansa a halin yanzu dai, shi ne neman hana Iran ci gaba da azurta sinadarin yurenuiyum da Kungiyar Hadin Kan Turan ke yi. A cikin tayin da suka yi mata, kasashen Birtaniya da Jamus da Faransa sun ce za su amince da amfani da tashoshin nukiliyan da Iran za ta yi wajen samad da makamashi, ta hannunka mai sanda. Sai dai su kasashen yamman ne za su dinga bai wa Iran din sandunan yureniyum da za ta bukata.

Amma a nata bangaren, Iran na matashiya ne da hakkin da take da shi, wajen azurta sinadarin yureniyum din da kanta, a matsayinta na wadda ta sanya hannu a kan yarjejeniyar nan ta hana yaduwar makaman nukiliya. To a nan ne rikicin ya barke. Saboda su kasashen Turan na shakku ne na cewa, idan aka amince wa Iran din sarrafa sandunan yureniyum din da kanta don yin amfani da su wajen samad da wutar lantarki kawai, babu tabbacin cewa ba za ta shiga yin amfani da su a fannin soji ba.

A cikin wannan yanayin rashin yarda da junan ne dai bangarorin biyu, za su halarci taron Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta kasa da kasa, wato IAEA a takaice, a birnin Vienna a ran laraba mai zuwa, don tattauna sabon rashin jituwar da aka samu. Bisa dukkan alamu dai, sai wannan rikicin ya karata a gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, musamman ma dai bayan da Iran din ta ba da sanarwar cewa, za ta fara ayyukan azurta sinadarin na yureniyum a masana’antarta da ke Isfahan, tun daga ran litinin, 8 ga wannan watan. Ana dai kyautata zaton cewa, jami’an Hukumar IAEA din za su kasance a birnin na Isfahan don sa ido kan yadda aikin zai gudana.

Kawo yanzu dai, Iran ba ta nuna wata damuwa ba game da barazanar da ake yi mata, ta kai batun gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Asefi ya bayyanar, babu abin da ke yi wa Jumhuriyar Islama ta Iran zafi a kan wannan batun. Kazalika kuma, yana ganin cewa babu wani abin da ke hujjanta matakin da ake niyyar dauka kan Iran din, ban da dai dalilan siyasa. Amma ya ce a ko yaushe, kasarsa a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da kasashen Turan.