1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici da tashe tashen hankula na ci gaba da tsananta a Darfur

November 20, 2006
https://p.dw.com/p/BubD

Masu sa ido daga kasashen ketare da kuma shugabannin yan tawaye a Sudan, sun shaidar da cewa tashe tashen hankula a yankin Darfur na ci gaba da tsananta.

A cewar daya daga cikin shugabannin yan tawayen, kwanaki uku da suka gabata, mutane sama da dozin daya ne aka kashe duk kuwa da yarjejeniyar tsagaitawa da bude wuta da aka cimma.

Wannan al´amarin dai yazo ne kwana daya, bayan dakarun kungiyyar Au sun zargi yan kungiyyar JANJAWED da take irin wannan yarjejeniya, ta hanyar kai hari na kasa da kuma sama.

Rahotanni dai sun rawaito kungiyoyin yan tawayen na bukatar aikowa da dakarun sojin Mdd izuwa yankin na Darfur, don gudanar da aikin kiyaye zaman lafiyar, to amma a waje daya mahukuntan na Sudan sunce hakan ba zata taba sabuwa ba, wai bindiga a ruwa.