Rikici a tsibirin Comores | Labarai | DW | 03.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici a tsibirin Comores

Rahottani daga birnin Monroni, sun ce ƙura ta lafa, a tsibirin Comoro, inda aka gwabza faɗa, daren jiya, tsakanin sojoji masu biyyaya ga shugaban yankin Anjouan, da na gwamnatin tarrayar tsibirin.

Majalisar dokokin tarrayya, ta zargi shugaba Mohamed Bakar,na Anjouan ta kitsa maƙarƙashiyar tada zaune tsaye cikin ƙasa.

Wannan saban tashin hankali ya ɓarke, bayan da kotun kolin Comoro, ta bayyana dokar kawo ƙarshen wa´adin mulkin shugaba Mohamed Bakar na yankin Anjouan.

A sakamakon wannan doka, shugaban haɗɗaɗiyar gwamnatin tsibirin, Ahmed Abdallah Sambi, ya naɗa magajin sa, a matsayin shugaban wucin gadi.

Ya zuwa yanzu, babu cikkaken bayyani, a game da yawan mutanen da su ka rasa rayuka, kokuma su ka ji raunuka.