1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici a Timo ta gabas

May 28, 2006
https://p.dw.com/p/BuwO

Ƙasar Australia, ta aika ƙarin dakarun kwantar da tarzoma a Dili, babban birnin Timo ta gabas, da ke fama da yake yake tsakanin matasa.

A halin yanzu, akwai a ƙalla sojojin 2250, daga ƙasashen Australia, New Zelandes, da Malaisia, wanda ke da yaunin maido doka, da oda a faɗin ƙasar baki ɗaya.

Faɗa, tsakanin matasa ɗauke da adduna, sanduna, da wuƙaƙe, gami da borin da wasu jami´an tsaro su ka tada,ya yi barazar kiffar da shugaban ƙasa Xanana Gusmao.

Wannan shine rikici mafi muni, da ƙasar ta fuskanta tun shekara ta 1999, da ta samun yancin kanta.

Ta la´akari da yadda, harakokin su ka tabarbare a Dili, Majalisar Ɗinkin Dunia, ta umurci jami´an ta, da su gama yanasu, yanasu, su fice daga wannan birni.