1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici a Somalia ya lafa

Ibrahim SaniJune 1, 2007

Yan gudun hijira a Somalia sun fara dawowa izuwa gida

https://p.dw.com/p/BtvR
sojin kiyaye zaman lafiya na kungiyyar Au
sojin kiyaye zaman lafiya na kungiyyar AuHoto: AP

Bayan da aka samu galabar shawo kann rikicin kasar Somalia, a yanzu haka yan gudun hijira na kasar sun fara dawowa izuwa gida.

A cewar hukumar kula da yan gudun hijira ta Mdd, kashi daya cikin hudu na wadanda suka yi gudun hijira dubu dari hudu ,a yanzu haka sun dawo izuwa birnin Magadishu.

Wannan yaki da aka gwabza tsakanin dakarun sojin kasar dake samun tallafin sojin Habasha da kuma dakarun kotunan islama, abu ne da a cewar hukumar kula da yan gudun hijirar yayi sular mutuwar mutane dubu daya da dari uku, banda wasu daruruwa da suka jikkata.

Game kuwa da halin da ake ciki yanzu, hukumar ta Mdd,tace da yawa daga cikin yan gudun hijirar da suka dawo izuwa kasar na fuskantar matsaloli na wahalhalun rayuwa na yau da kullum. A misali akwai matsaloli na rashin ingantacciyar wutar lantarki da karancin ruwan sha, da tarin shara da makamaman tansu, wadanda ke kawo barazana ga rayuwar mutanen.

A yanzu haka dai rahotanni sun shaidar da cewa, jami´an hukumar ta Mdd tuni suka sa ido a game da abin da kaje yazo na dangane da shigi da ficin yan gudun hijirar, don sanin irin matakan daya kamata a dauka na kara tallafa musu.

Tuni dai hukumar ta Mdd ta daukaka kira ga kasashe masu hannu da shuni, dasu kawo dauki dangane da ceto rayukan yan gudun hijirar da suka dawo gida, ta hanyar sake tsugunar dasu a gidajen su na asali.

To sai dai kuma duk da wannan hali da ake ciki na tsagaitawar bude wuta, da yawa daga cikin yan gudun hijirar sun ki su dawo izuwa gida. A cewar rahotanni da yawa daga cikin su na tsoron abin da ka iya tasowa.

Da yawa dai daga cikin ire iren wadannan yan gudun hijira na zaune ne a cikin dazuzzuka dake kudancin kasar ta Somalia, wadansu a karkashin bishiya wasu kuma a tantagaryar filin Allah ta´ala.

A yanzu haka dai a cewar bayanai hukumar kula da yan gudun hijirar na ci gaba da karbar yan gudun hijirar, duk kuwa da cewa akwai karancin abubuwan more rayuwa da aka tanar domin kula da lafiyar su. Babban dai abin yi a cewar masu nazarin abin da kaje yazo shine na shawo kann wannan rikici gaba dayan sa, wanda a cewar su yin hakan ne zai taimaka wajen dawo da wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali baki daya, a fadin kasar ta somalia.