Rikici a Pakistan | Siyasa | DW | 23.09.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikici a Pakistan

Waɗanda suka kai harin a birnin Islamabad, bisa dukkan alamu, burin su shine su ga bayan manyan shugabannin ƙasar ta Pakistan.

default

Ɓaragusan hotel ɗin Marriott a Islamabad bayan harin da aka kai kansa.

Hakan kuwa ya fito fili bayan da aka sami bayanin cewar harin shi kansa, ranar Asabar aka shirya kai shi, kamar yadda mashawarcin tsaro na gwamnati, Rehman Malik ya nunar, bayan jawabin farko na sabon shugaban ƙasa, Asif Ali Zardari, a majalisar dokoki, inda shi da sauran manyan jami'an ƙasar suka shirya haɗuwa a Hotel ɗin Marriot da yamma domin cin abinci.

Hotel ɗin mai suna Marriot nan ne aka shirya haɗuwar, inda shugaban majalisar dokoki ya shirya yiwa shugaban ƙasa da sauran jami'an siyasar ƙasar liyafa. Da farko mun amince da haka. Su kuma yan tarzoman sun san cewar shugaban ƙasar da Pirayimminista da shugaban majalisar dokoki da sauran dukkanin shugabanmnin kasar ta Pakistan zasu halarci wurin wannan liyafa.

Jim kaɗan kafin ´yan siyasar su haɗu ne jami'an tsaro suka yanke ƙudirin ɗage lokacin liyafar. Malik yace yana mamakin yadda har aka yi waɗanda suka shirya kai harin na ƙunar-baƙin-wake suka san wannan canji na lokacin shirya liyafar.

Har yanzu dai ana cikin wani hali ne mai matuƙar wahala a Pakistan bayan harin na yan tarzoma ranar Lahadi. A lardin arewa maso yammacin ƙasar ´yan tarzoma sun kama ƙaramin jakadan Pakistan, inda suke garkuwa da shi, bayan da ska kashe direban sa. Saboda matsaloli a tsaro a ƙasar ta Pakistan, kamfanin jiragen sama na Ingila, British Airways ya dakatar da zirga-zirga gaba ɗaya zuwa ƙasar, yayin da jami'an hukumar kuɗi ta duniya, wato IMF suka fice daga Pakistan ɗin cikin gaggawa. Tun da farko jami'an suka ce ƙasar dai tana fama da matsalar hauhawar farashin kaya da koma bayan tatalin arziki, saboda haka sun ziyarci kasar ne domin nazarin irin taimakon da take bukata. Kakakin kungiyar yan kasuwa da masu masana'antun Pakistan a Punjab yace:

Wannan hari na yan tarzoma abu ne da yi wa Pakistan mummunan illa fiye da kima, saboda babu sauran mai kasadar zuba jarin sa a Pakistan, muddin za'a ci gaba da fama da irin wannan barazana.

Wani ɗan Pakistan yace:

Tilas ne dukkanin jam'iyu su haɗa kansu, su yi namijin ƙoƙarin domin shawo kan manyan matsalolin mu, waɗanda sune koma bayan tattalin arziki da aiyukan tarzoma.

Wani kuma cewa yayi, kamata yayi al'umar Pakistan gaba ɗaya su haɗa hannu wuri guda domin adawa da manufofin Amerika a Pakistan, maimakon su riƙa yaƙi da junan su. ´Yan Pakistan da dama suna ganin Amerika da gwagwarmayar da take yi da aiyukan tarzoma sune manyan dalilin halin da Pakistan ɗin take ciki a yanzu. Gwamnati tana sane da cewar idan har ta kyale Amerika ta ci-gaba da farautar ´yan Taliban a lardin kudu maso yammacin ƙasar, hakan zai ƙara karfin hare-hare na magoya bayan ta a sauran yankunan wannan ƙasa. Duk da haka, gwmanatin tana sane da muhimancin yaƙi da aiyukan tarzoma. Saboda haka ne wani jami'in gwmanati yace: ko dai mu sami nasarar yakin mu kan aiyukan tarzoma, ko kuma mu mika kasar kai tsaye ga yan tarzoman kowa ya huta.

A halin da ake ciki kuma, shugaban ƙasa Zardari yace aiyukan tarzoma kamar yadda ƙungiyoyin al-Qaeda da Taliban suke tafiyar da su, daidai suke da cutar cancer dake addabar Pakistan, to amma yayi alƙawarin magance wannan cuta. Yace waɗannan mutane matsorata ba zasu hana mu tafiyar da aiyukan kyautata ƙasar mu ba ko kuma samun nasarar yaƙi da munanan ɗabi'un su.

Sauti da bidiyo akan labarin