1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici a Mogadiscio

July 27, 2007
https://p.dw.com/p/BuFN

A birnin Mogadiscio na ƙasar Somalia, a naci gaba da ɓarin wuta, tsakanin dakarun gwamnati dana kotunan Islama.

Rahottani daga ƙasar, sun ce a sahiyar yau, ƙarin mutane 5 sun rasa rayuka, a wata fito na fito tsakanin ɓangarorin 2 masu yaƙar juna.

Tashen-tashen hankulla sun kara tsamari a Mogascio, a daidai wannan lokaci, da taron haɗin ƙasa ke gudana.

Dakarun kotunan Islama sun yi watsi da kiran gwamnatin riƙwan ƙwarya, na halartar wannan taro, da aka fara tun ranar 15 ga watan da mu ke ciki.

Kazalika, sun sha alwashin ɗaukar dukkan matakan da su ka dace, domin tarwatsa taron da su ka ce haramtacce ne.

A ɗaya wajen kuma,komitin da Majalisar Ɗinkin Dunia ta girka, domin sa ido, ga takunkumin makamai da a ka laƙƙawa Somalia, ya nunar da cewa, wannan mataki bai anfana komai ba, domin makami masu yawa na shiga ƙasar a ɓanagaren iyarakar ta, da Erythera.

Komitin ya ce kussan dukkan wannan makami na zuwa ga dakarun kotunan Islama.