Rikici a Jan Massalacin Islamabad | Labarai | DW | 05.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici a Jan Massalacin Islamabad

A birnin Islamad na ƙasar Pakistan , wasu yan takife ɗauke da makamai, sun yi garkuwa da sauran almajiran da ke cikin jan massalaci.

Yan takifen kimanin su 30, sun yi watsi da kiran Abdul Aziz shugaban wannan massalaci, da ya yi shigar mata domin ficewa daga ciki, amma jami´an tsaro su ka gano shi.

Ya zuwa yanza akwai a ƙalla mutane dubu ɗaya, kann maza kann mata, da su ka yi saura a cikin massalaci .

Ranar talata da ta wuce a ka fara arangama tsakanin jami´an tsaro da wannan almajiran makarantun allo, da gwamnati ke zargi da yaɗa aƙidar yan taliban.

Baki ɗaya mutane 16 su ka rasa rayuka, sannan da dama su kam ji raunuka acikin arangamar.

Tun shekaran jiya, jami´an tsaro su ka yi wa massalacin zobe, tare da yin kira ga almajiran su fita daga cikin sa.

Kawo yanzu ɗaruruwa daga cikin su sun karɓi wannan kira.