1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici a Jamhuriya Demokradiyar Kongo

Jamhuriya Demokradiyar Kongo na shirin tsunduma cikin wani yanayin yaƙi, bayan bayana sakamakon zaben shugaban kasa zagaye na farko.

Rahotani daga Kinshasa baban birnin kasar sunce a yau ma ,saurari amen manyan-manayan bindogogi kusa da gidan mataikamin shugaban ƙasa bugu da ƙari ɗan takara Jean Piere Bemba, wanda zai je zagaye na 2, tare da shugaba mai barin gado Joseph kabila.

Wakilin Majalisar Dinkin Dunia a ƙasar yayi kira ga ɓangarori daban-daban da su daina tsokananar juna.

Ya kuma bukaci su hau tebrin shawarwari, domin warware rikicin ta hanyar tantanawa.

A nata gefe rundunar shiga tsakani ta ƙungiyar gamayya turai, ta ɗaura ɗamara , kazalika ta bukaci sojojin ta, dake kasar Gabon, su dawo Kinshasa, domin fuskantar saban rikicin da ya ɓarke.