1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici a Iraqi yayinda ake sa ran sanya hannu kan daftarin mulkin kasar a yau

Hauwa Abubakar AjejeAugust 25, 2005

Rikici ya barke tsakanin bangaroyin shia na Iraqi saoi kadan kafin majalisa ta amince da daftarin tsarin mulkin kasar

https://p.dw.com/p/BvaF
Magoya bayan Muqtada al-sadr
Magoya bayan Muqtada al-sadrHoto: ap

A safiyar yau din nan mazauna birninen shia dake kudancin kasar ta Iraqi sun bada rahotannin kone konen ofisoshi,a Amara kusa da birnin Basra an kasha wani dan sanda cikin fafatawa day an bindiga na kungiyar Muqtada as Sadr ta Mehdi da suka mamaye hedkwatar wata kungiya mai suna Badr cikin daren jiya.

Kungiyar ta Sadr ta bi sahun manyan malaman sunni tana mai nuna adawarta da daftarin tsarin mulkin kasar da har yanzu ake takaddama akansa,inda da dama suke ganin zai iya janyo rarrabewar kasar.

Kasar Amurka ta matsa da a amincewa da sabon daftari na mulkin kasar a matsayin daya daga cikin kaidojin da ta gindaya na janyewar sosojinta daga Iraqi,kodayake ta sanarda kara yawan sojojin 1500 a wani bangare na sojoji 20,000 da take niyar aikawa da su Iraqin domin sa ido akan kuriar raba gardama da zabe da zaa