Rikici a Gabacin Chadi
November 26, 2007Talla
Faɗa ya barke yau litinin a gabacin Chadi kusa da bakin iyakarta da Sudan a ɓangaren Darfur.Wannan faɗa ya barke ne bayan wasu ƙungiyoyin `yan tawaye biyu sun baiyana kawo ƙarshen yarjejeniyar tsagaita ɓude wuta a ƙarshen mako.Ma`aikatan agaji a yankin sun bada rahoton jin harbin bindigogi kusa da garuruwan Forchana da Hadjer Hadid inda yan tawayen suka shiga a ranar Asabar suka yi musayar wuta da dakarun gwamnati.