Rikici a gabacin Afghanistan tsakanin yanTaliban da sojojin NATO | Labarai | DW | 29.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici a gabacin Afghanistan tsakanin yanTaliban da sojojin NATO

Mutane da dama su ka rasa rayuka, a yayin da wasu su ka ji mummunan raunuka, a lokacin da aka gwabza wani ƙazamin faɗa tsakanin dakarun ƙungiyar Taliban da sojojin ƙasa da ƙasa , a gabacin Afghanistan.

A cewar sanarwar rundunar tsaro ta NATO, dakarun ta sun kai hari, a garin Asdadad, dake kussa da iyaka da Pakistan, domin tarwatsa wani gungun mayaƙan Alka´ida da na yan Taliban, da su ka capke wannan yanki.

Saidai ya zuwa yanzu, babu wata sanarwa daga ɓangaren yan Taliban da ta yi huruci a game da wannan labari.

A ɗaya wajen kuma, wani dan ƙunar baƙin wake,ya tarwatsa Bam a Lashkar Gah gap ga sasanin rundunar ƙasa da ƙasa ta yankin Helmand.

Jami´in tsaro ɗaya, tare da fara hulla 2, su ka rasa a cikin wannan hari.