1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici a Cote d'Ivoire

January 3, 2006

Har yau ana fama da tashe-tashen hankula a Cote d'Ivoire

https://p.dw.com/p/Bu2m

An yi bara kashi mai tsananin gaske a barikin sojan Akouedo dake kusa da birnin Abidjan a jiya litinin da sanyin safiya, kamar yadda rahotanni suka nunar, amma daga bisani hafsan-hasoshin sojan kasar Cote d’Ivoire janar Philippe Mangou ya ce kura ta lafa, an kuma samu kafar lafar da kurar rikicin, amma ya musunta jita-jitar da ake yadawa game da boren wani bangare na sojan gwamnatin kasar ta yammacin Afurka. An tsare fursinoni 32 a baya ga gawawwakin wasu dake cikin fararen kaya, wadanda ake kyautata zaton cewar wasu ne daga cikin masu alhakin kai harin ne dake sanye da kayan layu. Shugaba Laurent Gbagbo wanda ya kai ziyara barikin sojan yayi ikirarin cewar masu alhakin harin wasu ne daga ketare, wadanda kuma aka tara bayanai game da su. Kazalika, shi ma sabon P/M kasar Cote d’Ivoire Charles Konan Banny, wanda ke ziyarar birnin Dakar lokacin da abin ya faru, a cikin wani jawabin da yayi ta gidan telebijin, ya bayyana bakin cikinsa a game da yadda wasu mutane ke kokarin cimma burinsu da karfin bindiga a daidai lokacin da kasar ta dukufa wajen neman bakin zaren warware rikicinta da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin al’umarta.

Arangamar dai ta sanya al’amura sun tsaya cik a birnin Abidjan bayan da labari ya yadu tsakanin jama’a. Jami’an tsaro sun shingence titunan birnin na Abidjan, sannan unguwar Plateau dake cibiyar birnin. Tun dai abin da ya kama daga shekara ta 2002 kasar Cote d’Ivoire ke fama da rarrabuwa sakamakon yakin basasa da rashin jituwa ta siyasa. Kuma wannan harin, wanda yayi sanadiyyar rayukan sojoji uku da dakaru bakwai daga masu alhakin kai harin, kamar yadda rahotanni suka nunar, shi ne na farko tun bayan wani farmakin da aka kai kann wata babbar tasha ta ‚yan sanda a birnin na Abidjan a ranar daya ga watan desamban da ya wuce. Kawo yanzu kuwa ba wanda wani cikakken bayanin da aka samu a game da masu alhakinsa. Kazalika harin na jiya litinin ya zo ne kwanaki kadan bayan da sabon P/M Charles Konan Banny ya nada wakilan gwamnatinsa da ta hada da magoya bayan shugaba Gbagbo da abokan adawarsa da kuma tsaffin ‚yan tawayen da suka mayar da arewacin Cote d’Ivoire karkashin ikonsu tun watan satumban shekara ta 2002.