1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici a Chadi

Zainab A MohammadOctober 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bu58

Rahotanni daga kasar Tchadi na nuni dacewa yan adawa dake yankin arewa maso tsakiyar kasar ,sun karbe madafan ikon garin Goz Beida dake gabashin kasar ,amma sun fice daga cikinsa da safiyar yau litinin.A jiya lahadi ne dai yan adawan suka bada sanarwar karbe wannan gari,amma daga baya dakarun gwamnati sun afka musu.Rahotannin kungiyoyin bada agaji dai ,na nuni dacewaharkokin tallafi a samsanonin yan gudun hijira na Sudan sun koma kamar da.Acheikh Ibn Oumar ,dake jagorantar kungiyoyin yan adawa dake yankin,ya gabatar da sanarwar karbe madafan ikon Goz Beida a jiya lahadi.To sai kawo yanzu babu sanarwa dangane da wadanda suka jikkata daga bangarorin biyu,sakamakon wannasn arangama.Garin Goz Beidoa dai nada sansanonin miliyoyin yan gudun hijira da suka fito daga Darfur din kasar Sudan.