1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici a birnin Mogadiscio na Somalia

May 8, 2006
https://p.dw.com/p/BuzG

A ƙalla mutun ɗaya ya rasa ran sa , sannan mutane da dama, sun ji raunuka, a birnin Mogadiscio na kasar Somalia, a sakamakon arangama tsakanin kungiyoyin sa kai, da dakarun kotunan musulunci, na wannan kasa.

Duk da cewar babu cikkaken bayani, a game da ɓarkewar rikicin, a na sa ran, ya samo asuli, daga adawar da ta haɗa kotunan musulunci na kasa, da shugabanin kungiyoyin sa kai, a kan jagorancin Mogadiscio, babban birnin Kasar.

Tun watan februaru da ya wuce, an yi kwanaki na ɓarin wuta, tsakanin dakaraun kotunan musulci na kasa, da kungiyoyin sa kai, bayan da wannan kungiyoyi su ka zargi alkalai ,da bada mafaka, ga membobin Alka´ida, daga ƙasashe ƙetare a Somalia.

Rikicin da ya biwo baya, ya jawo assara rayuka kussan 90 a babban birnin.

Tun bayan wannan rikicin limmamai da sauran mallummai masu faɗa a ji, su ka yi kira, ga magoyan bayan su, da su tashi tsayin daka, domin kariyar addini, da ƙasar Somalia daga ƙungiyoyin tawaye.

Somalia, na fama da rikicin tawaye tun shekara ta 1991, bayan kifar da Shugaba Mohamed Siyad Bare, daga karagar mulkin kasa.