1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici a Afghanistan

A kalla mayakan taliban 25 su ka rasa rayuka a cigaba da aranmaga da dakarun ƙasa da ƙasa a yanƙin Helmand da ke kudancin ƙasar Afghanistan.

Sojojin Ƙungiyar tsarao ta Nato, tare da haɗin gwiwar dakarun gwamnatin Afghanistan na fuskantar turjewa mai tsanani daga mayakan Taliban a wannan yanki.

Tun ranar 6 ga watan Maris da ya gabata dakarunkasa da ƙasar su ƙadammar da wani gagaramin yaƙi da zumar ƙaƙƙabe yan taliban daga yankin, to saidai ya zuwa yanzu, babu alamun cimma nasara.

Kussan a ko wace rana tarkunan dakarunTaliban, na capke sojojin ƙawancen.