1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikice rikicen Iraki

Zainab A MohammadApril 27, 2006
https://p.dw.com/p/Bu0T
shugaba Talabani da premier al-Maliki na Iraki
shugaba Talabani da premier al-Maliki na IrakiHoto: AP

A yayinda manyan jamian kula da harkokin ketare na Amurka ke cigaba da rangadin aiki na bazata da suka fara a jiya a Iraki,harkoki na tashe tashen hankula daga harin yan yakin sunkuru na cigaba dayin kamari.

Da sanyin safiyar yau ne dai wasu yan bindiga dadi suka bindige yar uwar mataimakin shugaban kasa daga darikar sunni Tareq al-Hashemi,a wani abunda ke zama sabon babi a harkokin siyasar kasar ta Iraki.

Malama Mayssun Hashemi dai ta gamu da ajalinta ne ,alokacin da wadannan yan bindiga dadi sukayiwa motar da take tafiya ciki kwanton bauna,a unguwar Al-Ilam dake bagazan,inda akayiwa motar wanta da harsashin dayayi sanadiyar ranta dana matukin motar ta.

Gidan talabijin mallakar jammiyar islama ta mataimakin shugaban kasa Hashemi dai,ya katse watsa shirye shiryensa nan take,domin nuna yadda harsashi ya lalata yar uwar mataimakin shugaban kasar da kuma motar da take ciki daya kasance tankar an masa shape ne da jinni.

Rahotanni dai na nuni dacewa kimanin harsashi 32 biyu akayi amfani dasu wajen harbin wannan baiwar Allah da Drebanta.Idan baa mance ba a farkon wannan wata nedai aka bindige,dan Uwan Tareq al-hashemi.

A makon daya gabata nedai aka zabi Hashemi a matsayin mataimakin shugaban kasa na farko daga darikar Sunni,tare da Jalal Talabani a matsayin shugaban kasa,kana Adel Abdel Mahdi,zai kasance mataimakin shugaban kasa na biyu.

Akan ire iren wadannan tashe tashen hankula ne shugaban yan darikar Shia na Irakin,Ayatollah Ali al-Sistani,ya bukaci sabuwar gwamnati da zata haye karaga,data dauki matakai na warwagaza harkokin yan ta kifen kasar wadanda ke neman jefa kasar yakin basasa.

Ali al-Sistani ,mutumin dake zama mafi daraja a kasar,ya fadawa zababben Prime minister Jawad al-Maliki a wata ganawa da sukayi a harabarsa dake Najaf cewa,dole ne a kwace makaman yan yakin sari ka noken,domin a hannu dakarun gwamnati ne kadai makamai ya dace su kasance.

A yanzu haka dai al-Maliki,wanda aka zaba a matsayin sabon Premiern Irakin a makon daya gabata na fuskantar matsin lamba na gaggauta kafa gwamnatin Hadaka ,wanda ake ganin zai kawo karshen tashe tashen hankula,da ake zargin cewa yan darikar shia dake maaikatar harkokin cikin kasa na Irakin n eke ingizawa.

To sai dai a yayinda alumomin irakin ke cikin zulumi na ire iren wadannan asaran rayuka da akeyi a kowane wayewan gari,sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice dana tsaro Donalds Rumsfeld,sun yabawa hazakar sabbin shugabannin Irakin,tare da kira agaresu dasu samara da gwamnati mai nagarta da zata wakilci yan kasar baki daya.

Rice ta fadawa taron manema labaru a ofishin jakadancin Amurka dake Bagadaza cewa ,alumomin kasar zasu maraba da sabuwar gwamnatin ne kadai ,idan sun hakikance cewa zasu share musu hawaye bisa,wanda ta bayyana shi da kasancewar babban kalubale ne a gaban shugabannin.

To sai dai a wannan yanayi da Irakin ta tsinci kanta ciki,babu wanda yasan yadda zata kasance,sai dai fatan cewa kwalliya zata biya kudin sabulu.