1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikice rikicen Afrika na bukatar tallafin gaggawa na kasashen duniya

Zainab A MohammadMay 11, 2005

Yankin arewacin Uganda na cigaba da kasancewa cikin halin niyasu,dangane da hare haren yan tawayen LRA

https://p.dw.com/p/Bvc4
Hoto: AP
Hukumar agajin gaggawa na majalisar dunkin duniya tayi kira ga komitin Sulhun Majalisar,daya gaggauta daukan matakan kawo karshen rikicin dake addaban arewacin Uganda.

Arewacin Ugandan dai na fuskantar tashe tashen hankula,sakamakon adawa da gwamnati tun daga shekarata 1988.Yanzu haka dai kimanin mutane million 1 da dubu dari 4 suka yi gudun hijira sakamakon rikicin yan tawayen da ake kira Lords resistance Army ko kuma LRA,a takaice,inji Ja Egeland dake jagorantar hukumar agajin gaggawa ta mdd dake dake Uganda.

Gabanin taron dazai gudana a asurce na majalisar inda ake kyautata zaton zai bukasci wakilai su mayar da hankali kan rikice rikicen Afrika,Egeland ya fadawa taron manema labaru cewa, a yan makonnin da suka gabata sun samu rahotannin yadda akewa fararen hula yankan rago,ayayinda ake nakasa wasu ta hanyar yanke musu bangarorin jikinsu.

Ya bayyana taaddancin kungiyar yan tawayen arewacin Ugandan da kasancewa mafi muni a nahiyar Afrika,amma injishi sabanin rikicin lardin Darfur ,duniya tayi watsi da laakari da matsananci hali da yankin arewacin Ugandan ke ciki shekasra da shekaru.

A dangane da hakane ya kira komitin sulhun da kuma wadanda ke fada aji dangane da wannan rikici,domin jaddada musu cewa akwai bukatar warware wadannan rikice rikice dake addaban alumma,domin azabar ta kazanta.

Banda hare hare da mayakan Ugandan keyi,sukan afkawa sansanin yan gudun hijira ,tare da sace yayansu da kuma tilastawa yanyansu maza shiga sojin dole,a inda sukan dauke yara matan domin yi musu fyede da kuma bauta.

Egeland ya kara dacewa a yanzu haka akwai kimanin yara kanana dubu 42,wadanda kan tsere cikin dare daga sansanin da suke zube da kuma kauyuka,zuwa wasu wurare da suke ganin yafi tsaro,musamman titunan manyan garuruwa suna kwana,domin tsira daga azabar wadannan azzaluman yan tawayen.

Tun daga shekarata 1988 nedai kungiyar yan tawayen LRA ke yakan gwamnatin shugaba Yoweri Museveni na Uganda ,daga Arewacin kasar da kuma kudancin Sudan ,da nufin kifar da wannan mulki,tare da maye gurbinsa da wanda zai dogara da dokoki goma na Attaura.

Dukkan yunkuri da akayi na warware wannan rikici a baya yaci tura,ayayinda ake cigaba da rashin jituwa da amintan juna tsakanin bangarorin adawan biyu.

Jamiin dai yayi wannan kiran ne da nufin jan hankalin duniya zuwa kan rikice rikice dake cigaba da addaban sassa daban daban na Afrika,domin nan ne keda babban kalubale a halin yanzu.

Mr Egeland wanda fuskarasa ta kasance sananniya a akwatunan talabijin din jamaa da dama tun bayan Balain tsunami a watan Disamba,yace sakonsa shine dukkan kudi da aka kashewa nahiyar Afrika ba asara bane,domin akwai nasarori da aka samu wajen sake ginin kasashe,kamar su Angola da Saleon,bayan tsawon shekaru nay akin basasa.