Rikice rikice a yankin Palasdinawa na karuwa | Labarai | DW | 22.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikice rikice a yankin Palasdinawa na karuwa

An kashe wani dan kasar palasdinu a wani harin taho na taho da ya sake tashi a birnin Gaza.

A cikin daren jiya ne aka rika musanyar wuta,kusa da gidan shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas tare da na ministan harkokin waje Mahmoud Al-zahar.

Rahotani sun bayyana cewa wannan fadan ya barke ne tsakanin magoya bayan Abbas na kungiyar adawa ta Fatah da na Hamas mai mulki,bayan wasu yan bindiga sun saci wasu yan kungiyar Hamas su biyu,tare ma da wani jami in tsaro na Al-zahar.

A wata sabuwa kuma yan ta adda a kasar sun harba wani roka a tsabirin Negev da ke kudancin Israila,bayan tsawon wata guda na tsaida hari da aka cimma tsakanin kasashen biyu