Rijiyoyin hakar zinariya a Najeriya: Aiki mai kashe yara kanana
Daruruwan yara suke aikin wahala a rijiyoyin hakar zinariya a Najeriya. A watannin baya yara 28 suka mutu daga cutar gubar dalma. Tun bayan wannan hadari babu abin da ya canza. Wakilin DW Adrian Kriesch ya ziyarci wurin.
Guba mai kisa
Har yanzu daruruwan yara suke aikin tona kasa suna neman zinariya a Najeriya. A watan Mayu yara 28 suka mutu, duka masu shekaru kasa da shida. 'Yan uwansu ne suka kai duwatsu masu guba gida inda aka yi amfani da magunguna masu hadari domin cire zinariya daga duwatsun. Komai kankantar magungunan suna iya kashe kananan yara da ba su kai shekaru shida da haihuwa ba.
Rayuwar yau da kullum mai muni
Ga kananan yara, taba tufafi masu guba kadai ya isa shiga mummunan hadari. Watanni uku bayan hadarin da ya kashe yara 28, halin da ake ciki a inda abin ya faru yana ci gaba da kawo damuwa. Yara da yawa masu aiki a rijiyoyin zinariyar ba su wuce shekaru shida da haihuwa ba. Sukan yi aiki tun daga wayewar gari har zuwa faduwar rana suna neman zinariya. Ba a cika ganin manya suna wannan aiki ba.
Gubar dalma mai kisa
A yunkurin kyautata hanyoyin da yaran za su kare kansu ne ya sanya wata kungiyar agaji take aikin wayar da kai a kauyen. Ana sanar wa yaran cewar bai kamata su rika tafiya gida da tufafin da suke aiki da su ba, kada kuma su rika amfani da magunguna masu hadari, sannan su kauce wa rijiyoyi masu hadari. Amma ma'aikatan agajin ba sa iya hana yaran wannan aiki gaba daya.
Rijiyoyin hakar zinariya maimakon karatu
Kamar dai wannan yarinya: "Iyayena suna bukatar kudin da nake samu", inji Habi. Ita kanta ba ta san shekarunta na haihuwa ba, amma yanzu shekaru biyu kenan tana aiki a rijiyar hakar zinariya. Duk da haka, ba kamar takwarorinta masu yawa ba, Habi akalla ta kan je makaranta jefi-jefi.
Tafiya mai wahala
Rijiyoyin zinariya masu yawa suna jihar Niger ne. A lokacin damina yankin da suke ya kan yanke da sauran jihar baki daya. Hanya daya da ke isa can ruwan sama kan maida ita kamar kogi. Motoci ba sa iya wucewa, babura kuma sai dai a tura su. Sai an yi tafiyar sa'o'i hudu kafin a isa hanya mai kyau da ke isa kauyukan yankin. Wannan hali ya nuna yadda gwamnati ta kasa a aikinta.
"Me kuke nufi da aikin kananan yara?"
Bayan mutuwar yara 28, an kafa hukumar da za ta yi binciken gubar dalma. To amma a Kagara, hedkwatar karamar hukumar yankin, mahukunta sun musunta aikin kananan yara: "Me kuke nufi da aikin kananan yara?", inji shugaban hukumar binciken da aka kafa, Alhaji Abdullahi Usman Katako. Ya nuna cewar ba zai yiwu a dauki matakai na kariya masu yawa ba lokacin damina saboda rashin kyawun hanyoyi.
Babu hanyoyin kula da lafiyar yara
Misalin kashi 80 cikin 100 na yaran da ke aiki a rijiyoyin suna dauke da gubar dalma, amma babu isassun likitoci da za su duba lafiyarsu. A kusa da rijiyoyin zinariyar an tanadi dakin likita na tafi-da-gidanka. Likitan da ke wurin bai koyi aikin likita ba, in banda horon gaggawa da ya samu a babban birnin yankin. Saboda haka ake kai yara masu yawa manyan garuruwan yankin domin yi masu magani.
Azuzuwa biyar, dalibai 143, malami daya
A makarantar kauyen Shikira, malami daya ne yake karantar da yara 143, a dukkanin manhajojin karatu. "Sau tari yaran sukan ki zuwa makaranta, su je neman zinariya", inji Abdullahi Garba. Iyaye masu yara ba sa iya sayen kayan makaranta, amma a maimakon haka sukan tura 'ya'yansu zuwa rijiyoyin hakar zinariya. "Ina bukatar taimako yadda zan dakatar da wannan hali".
Ana bude karin rijiyoyi maimakon a yi gyara
Dan jarida Arukaino Umukoro, ya gabatar da rahoto jim kadan bayan mutuwar yaran daga cutar gubar dalma cikin jaridar da ita ce mafi girma a yankin. Amma tun bayan wannan lokaci babu wani canji da aka samu. A daura da haka ma, ana bude karin rijiyoyin hakar zinariya fiye da yadda ake da su a da. Omukoro ya ce; "Gwamnati tilas ta nemar wa yaran wani abin yi dabam, ta kara yawan jari a fannin ilimi."