1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rigingimu na haddasa kwararar 'yan gudun hijira a Najeriya

June 26, 2012

Dubban mutane na tserewa daga gidajen su a jihohin Borno da Yobe saboda tashe-tashen hankulan da ke ci gaba da lamushe rayukan al’umma musamman a garuruwan Maiduguri da Damaturu.

https://p.dw.com/p/15Lkk
People flee with their belongings from a riot affected area in Kaduna, Nigeria, Friday Nov. 22, 2002. Over 100 people have been killed in riots in Kaduna that started after a newspaper suggested that if Prophet Muhammed was still alive he may have chosen his bride from the contestants of Miss World beauty pageant who are presently in Nigeria. (AP Photo/Saurabh Das)
Hoto: AP

Akwai wasu al'ummomin da dama da suka nemi mafaka kodai a jihohi da garuruwa maƙobta inda wasu suka nemi matsugunai na ‘yan gudun hijira ko kuma makarantun firamare gwargwadon iko da halin da suke da shi.

Yanzu haka unguwanni da dama a Maiduguri sun zama kufayi saboda yadda mazauna unguwannin suka ƙaurace musu.

Tuni kuma wasu jihohin suka fara kwashe ɗaliban su dake a manya da ƙananan makarantun a wannan jihohin don gudun abinda ka iya samun su ganin hare-hare da kuma matakan magance su, na ƙara zafafa.

Wane hali waɗanan al'umma da suka tsere daga garuruwan suke ciki tambayar da na yiwa Hajiya Fatima kenan wadda ta ce ko shakka suna cikin mawuyacin hali na rashin sanin makomarsu.

Jami'a na tilasta wa mutane barin gidajensu

Ƙungiyoyin kare hakkin bani Adama dai na zargin jami'an tsaro da hukumomi tilastawa mutane barin matsugunansu saboda matakai da suke ɗauka, kamar yadda Abdullahi Muhamad Inuwa shugaban ƙungiyar tabbatar da adalci tsakanin al'umma a tarayyar Najeriya yayi nunar.

A Damaturu fadar gwamnatin jihar Yobe ma ɗaruruwan mazauna garin sun tsere saboda tashin bama-bamai da kuma matakai da ake ɗauka na daƙile hare-haren.

Sai dai kakakin gwamnan jihar Abdullahi Bego yace lokaci yayi da al'ummomin za su dawo gida saboda an samu zaman lafiya a garin sanadiyyar matakai da gwamnatin jihar ta ɗauka na tabbatar da tsaro.

**FILE** Chadian refugees walk inside a refugee camp at the border town of Kousseri, Cameroon, in this Thursday, Feb. 7, 2008 file photo. Tens of thousands of people fled when rebels attacked the capital of Chad this month, and about 3,000 ended up in the Nigerian border post of Ngala, two countries away from home _ the farthest-flung outpost in an archipelago of camps linked to the strife in Sudan's Darfur region.With the establishment of the camp at Ngala and one for 30,000 people to the east in Kousseri, Cameroon, on that country's border with Chad, those homeless in the Sudan-Chad conflict are now sheltering in five countries: Sudan, Chad, Central African Republic, Cameroon and Nigeria. (ddp images/AP Photo/Sunday Alamba)
Hoto: AP

An fara samar wa mutane abubuwan sauƙaƙa rayuwarsu

Haka kuma gwamnatin jihar ta samar da motocin safa da za su sauƙaƙe wahalhalun sufuri da al'umma suke sha sanadiyyar haramta amfani da babura a wannan gari da kuma samar da motocin safa ga makarantun sakandare gami da tallafi da ake baiwa ɗaiɗaiku da ƙungiyoyi.

Ita ma gwamnatin jihar Borno tace tana iya ƙoƙarinta na samar da yanayi da al'umma za su dawo gidajensu don ci gaba da harkokin su na yau da kullum.

Mawallafi: Aminu Suleiman Mohammed
Edita: Mohammad Nasiru Awal