Rigingimu a rana ta farko a yakin neman zabe a Kongo | Labarai | DW | 30.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rigingimu a rana ta farko a yakin neman zabe a Kongo

A rana ta farko a yakin neman zabe a kasar Janhuriyar Demukiradiyya Kongo, dakarun tsaro sun harbe akalla mutane 10 har lahira yayin wata zanga-zangar nuna kyamar gwamnati a birnin Matadi. An jiyo haka ne daga ofishin wakilan MDD wato MONUC dake Kongo. Wani kakakin MONUC ya ce wani dan sanda daya ya rasa ransa a lardin Bas. A kuma babban birnin kasar wato Kinshasa ´yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa akan wani gungun masu zanga zanga. A zaben na gama gari wanda shi ne irin sa na farko da za´a yi a Kongo a cikin shekaru 40, KTT ta girke dakarun ta a kasar bayan neman yin haka da MDD ta yi. Jamus ta ba da gudunmawar sojoji kusan 800 ga rundunar ta kungiyar EU.