1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Riga kafin cutar shan inna ga Afirka

October 27, 2010

Hukumar lafiya ta duiniya ta ce yara miliyan 72 ne za su sami allurar riga kafin cutar shan inna a wannan makon

https://p.dw.com/p/PolC
Riga kafin cutar shan innaHoto: AP Photo

Hukumar kula da lafiya a duniya wato WHO ta sanar da cewar, kasashen Afirka 15 ne za su amfana da wani shirin yiwa kananan yara miliyan 72 allurar riga kafin cutar shan inna a wannan makon. Rod Curts, kakakkin hukumar a hedikwatar ta dake birnin Geneva, wanda ya sanar da hakan, ya ce masu gudanar da aikin kimanin dubu 290 ne za su bi gida gida domin yiwa kananan yaran da shekarun su ya gaza biyar allurar. Wannan gangamin yaki da cutar shan inna wanda ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya dai, kasashen yankin yammacin Afirka ne za su fi cin gajiyar sa, ko da shike kuma za'a fadada aikin ya zuwa kasashen Sudan da kuma Chadi. Wannan kuma shi ne karo na ukkun da aikin ke gudana a nahiyar Afirka cikin wannan shekarar kadai.

Nijeriya, wadda ita ce kasar Afirka daya tilon da bata taba kawar da cutar ba a cikin ta, a makon jiya ne ta yiwa kananan yara kimanin miliyan 29 allurar, kuma a yanzu alkaluma na nuni da cewar, ta yi nasarar kawar da kashi 98 cikin 100 na cutar a tsakanin al'ummomin ta. Sai dai kuma kakakin hukumar kula da lafiya ta duniya Mr. Curts ya ce tilas ne a yi namijin kokari a nahiyar Afirka musamman a kasashen Angola da jamhuriyyar dimokradiyyar Kongo, inda yara 48 cikin 58 da suka kamu da cutar a watanni shidan da suka gabata ke zaune.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu