1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Riek Machar ya zama sabon mataimakin shugaban Sudan ta Kudu

Kamaluddeen SaniApril 27, 2016

A ranar Talatar nan ce aka rantsar da tsohon jagoran 'yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar mukamin mataimakin shugaban kasa bayan da ya koma gida tare da shiga cikin gwamnatin akarkashin yarjejeniyar zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/1IdFG
Südsudan Riek Machar Salva Kiir
Hoto: picture-alliance/AP Photo/P. Muller

Hakan dai na zuwa ne bayan da dukkanin bangarorin biyu wato tsakanin tsohon dan tawayen da kuma shugaban kasar Salva Kirr suka kai ga cimma daidaito domin samun dorewar zaman lafiya a kasar.

Kazalika Sabon mataimakin shugaban kasar ya kuma godewa Shugaba Salva Kirr a bisa na dashi mukamin na biyu a kasar data dauki tsawon lokaci tana fama da rikice rikece tsakanin bangarorin biyu.

Shirin yarjejeniyar tsagaita wutar da Majalisar Dinkin Duniya take shiga tsakani shine ya bayar da damar rantsar da Riek Machar a matsayin sabon mataimakin shugaban kasa gami da girka sabuwar gwamnatin hadin gambiza.

Tun dai a shekara ta 2013 sai da Riek Machar ya taba zama matimakin shugaban kasa kafin kasar ta Sudan ta Kudun ta fantsama cikin yakin basasar daya tilastawa daruruwan 'yan kasar neman mafaka a makwafciyar kasar ta Sudan .