Riek Machar ya sauka a birnin Juba
April 26, 2016Jagoran adawa a kasar Sudan ta Kudu ya Riek Machar ya sauka a birnin Juba a ranar Talatan nan bayan lokaci mai tsawo da aka dauka ana dakon ganin wannan rana da aka dade ana ta dagewa, abin da ke jawo tsaiko a shirin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla wacce ake fatan za ta kawo karshen watanni 28 da aka yi ana fafatawa tsakanin dakarun sojan gwamnati masu mara baya ga shugaba Salva Kiir da na 'yan tawaye da ke mara baya ga Riek Machar.
'Yan jarida dai sun bayyana cewa Mista Machar ya sauka a birnin na Juba ne cikin jirgin sama mallakin Majalisar Dinkin Duniya. An dai tsara cewa bayan Machar ya sauka a birnin na Juba bayan ya baro garin Gambella na kasar Habasha ba da dadewa ba ne za a rantsar da shi a matsayin mataimakin shugaban kasa kana daga bisani ya yi jawabi ga dandazo na magoya baya.