1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Riek Machar na shirin komawa Sudan ta Kudu

Abdourahamane HassaneApril 1, 2016

Sudan ta Kudu ta shaida wa kwamitin tsaro na MDD cewar sojojin da ke yin biyaya ga jagoran 'yan tawayen Riek Machar za su isa a Juba babban birnin ƙasar nan da lokaci kaɗan

https://p.dw.com/p/1INkM
Südsudan Rebellenführer Riek Machar
Hoto: Reuters/G. Tomasevic

Zuwan na 'yan tawayen zai ba da damar komawar Riek Machar a birnin Jubar daga inda yake gudun hijira a Habasha, domin kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa da shi da shugaba Salva Kiir. Kamar yadda yarjejeniya zaman lafiyar da aka cimma a cikin watan Augusta na shekarar bara ta amince da shi.

Yarjejeniyar zaman lafiyar ta tanadi raba iko tsakanin shugabannin biyu har na tsawon watannin 30 kafin shirya sabbin zaɓɓuɓuka. Tun farko Riek Machar na riƙe da matsayin matamaikin shugaban ƙasa kafin a samu rashin zutuwa tsakaninsa da shugaba Salva Kiir.