1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rice tana Beirut

July 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bu65

Wani jirgin yaki na dakarun Izraela ya tarwatse akan iyakar Izraela da Lebanon ta arewaci,yankin da dakrun izaraelan ke cigaba da arangama da a tun makon daya gabata.Kakakin dakarun na Izarela yace jirgin yakin nasu ya fado ne kusa da garin Yiron,mai tazarar km da dama daga kann iyakar kasashen biyu.Sai dai a yau din ne kuma sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice ta isa birnin Beirut din kasar ta Lebanon a wata ziyarar bazata a yau.Rice ta isa Beirut din ne da jirgi kirar Ungulu daga tsibirin Cyprus,a wani abunda aka bayana da kaddamar da rangadin aiki,akokarin Amurka na ganin cewa an ceto yankin gabas ta tsakiya daga fadawa yaki.Daya daga cikin jamian dake masta rakiya a wannan ziyara dai,ya sanar dacewa,Condoleeza Rice zata sanar da tallafin Amurkan wa Lebanon.