Rice ta isa a Isra´ila a matakin farko na rangadin yankin GTT | Labarai | DW | 13.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rice ta isa a Isra´ila a matakin farko na rangadin yankin GTT

An rawaito sakatariyar harkokin wajen Amirka C-Rice tana cewa shugaba GWB ne ya ba da umarnin kai samame akan wuraren sojojin sa kai na Iran dake cikin kasar Iraqi. A cikin wata hira da jaridar New York Times Rice ta ce shawarar kai samame a cibiyoyin Iran na daga cikin matakan soji da ake dauka a fadin Iraqi baki daya. Gwamnatin Bush na zargin Iran da taimakawa sojojin sa kai na ´yan shi´a da kudi da kuma makamai. A halin da ake ciki sakatariyar harkokin wajen ta Amirka ta isa kasar Isra´ila, matakin farko na wani rangadin kasashen yankin GTT, da nufin farfado da shirin wanzar da zaman lafiya tsakanin Isra´ila da Falasdinawa. Rice zata kuma ziyarci kasashen Masar, Jordan, Saudiyya da kuma Kuwaiti.