1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rice ta fara wata ziyarar ba zata a Iraki

November 11, 2005
https://p.dw.com/p/BvLa

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta isa kasar Iraqi a wata ziyara ta ba zata. Rahotannin da ba sa sabawa juna sun ce Rice ta sauka a birnin Mosul dake arewacin Iraqi. Da farko ta halarci wani taro ne a Bahrain inda aka tattauna dangane da ci-gaban mulkin demukiradiyya a yankin GTT. A lokacin da ta sauka a Mosul Rice ta yi kira ga al´umomin Iraqi da su kawad da bambamce bambamcen da ke tsakanin su gabanin zaben ´yan majalisar dokokin da zai gudana a cikin watan desamba. Sakatariyar harkokin wajen ta Amirka na wani rangadin yankin GTT ne, wanda zai kai ta Isra´ila da kuma yankin Falasdinawa bayan da ta fara yada zango a Bahrain.