Rice ta ce kada a kula da barazanar hukumomin Iran | Labarai | DW | 05.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rice ta ce kada a kula da barazanar hukumomin Iran

A dangane da takaddamar da ake yi akan shirin nukiliyar Iran, sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta yi kira da kada a ba da muhimmanci sosai ga barazanar dake fitowa baya bayan nan daga birnin Teheran. Rice ta fadawa gidan telebijin Amirka cewa Iran ta dogara kacokan akan kudaden da take samu wajen sayar da mai, saboda haka kasar zata fuskanci manyan matsaloli idan ta daina sayar da mai ga kasashe wajen. A jiya lahadi limamin limaman Iran Ayatollah Ali Khameni yayi barazanar cewa duniya zata fuskanci matsalar makamashi, idan aka kaiwa kasar hari. Ayatollah Khameni ya ce kasar sa zata kawo babban cikas ga harkar samar da mai a yankin Golf.