Rice da matsayin Amirka. | Siyasa | DW | 08.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rice da matsayin Amirka.

A ziyarar da take kaiwa a nahiyar Turai, sakatariyar harkokin wajen Amirka, Condoleeza Rice, tana ta yunkurin kare kasarta daga sukar da ake yi mata ta gallaza wa fursunoni. Wasu jawaban da ta yi sun saba wa matsayin fadar White House a kan wannan batun.

Condoleeza Rice

Condoleeza Rice

Kawo yanzu dai, mahukuntan birnin Washington ba su ce uffan ba, a kan jawaban da sakatariyar harkokin wajen Amirka, Condoleeza Rice ta yi, game da zargin da ake yi wa jami’an tsaron kasar, na azabtad da fursunonin da suke tsare da su. Wasu masharhanta dai na ganin cewa, sakatariyar harkokin wajen ta yi wata katobara, saboda bayananta sun sha bamban da na shugaban Amirkan George Bush a kan wannan batun. A cikin wani jawabin da ta yi a kasar Ukraine jiya, Rice ta nanata cewa, ko’ina Amirkawa suke a duniya, ba su kubuta ba daga ka’idojin nan na Majalisar dinkin Duniya, wadanda suka haramta gallaza wa fursunoni. Da can dai shugaba Bush na Amirka, ya fara bayyana cewa dokar haramta gallaza wa fursunonin, bai shafi Amirkawan da suke aiki a ketare ba. To wadannan bayan guda biyu da ke saba wa juna dai, suin janyo rudami ga jami’an fadar White House a birnin Washington.

A Amirkan da kanta ma dai, an fara samun karin yawan `yan majalisar dattijai wadanda ke kokarin gabatad da wata doka, wadda za ta hana azabtad da fursunoni a cikin kasar. Sai dai ofishin mataimakin shugaba Amirkan da fadar White House ne ke ta daddage wa shirin a halin yanzu. Amma duk da hakan, akwai alamun da ke nuna cewa, Sanata John McCain, dan jam’iyyar Republicans, wanda ya jagoranci gabatad da kundin dokar zai sami rinjayin `yan majalisar dattijan, wadanda za su goyi bayan shirin. Kazalika kuma ana ta kara samun masu sukar manufofin gwamnatin Amirkan a cikin gida da kuma ketare, musamman ma dai a nahiyar Turai. Dalilin da ya sa kuwa ke nan, Condoleeza Rice ke kai ziyara a nahiyar a halin yanzu, a wani yunkuri na kare kwarjinin kasarta da ke ta kara dusashewa a bainar jama’a.

Masu sa ido kan harkokin siyasar Amirkan dai na nuna shakku ga nasar da Rice ke fatar samu a wannan ziyarar tata a Turai. Richard Falkenrath, wani tsohon mai bai wa shugaba Bush shawara a kan hartkokin siyasa, ya bayyana cewa:-

„Ko da jami’an siyasan Turai da kuma jama’arta sun ji dadin jawaban da Rice za ta bayar, ina tantama ko za su amince da su.“

Burin da aka tanadi cim ma a wannan ziyarar ta Rice a Turai, shi ne inganta huldodi tsakanin kasashen nahiyar Ruran da Amirka. Amma labarin jigilar fursunoni da kungiyar leken asirin Amirkan, wato CIA ke yi a nahiyar Turan ya lahanta duk wannan yunkurin da sakatariyar harkokin wajen ke yi. Sai dai, a ganin Falkenrath, wannan sabanin da aka samu na wucin gadi ne. Akwai bangarori da dama, da har ila yau jami’an Amirka da na nahiyar Turai ke aikin hadin gwiwa a cikinsu:-

„A lokuta da yawa, Amirka na samun hadin kan wadannan kasashen a fautukar da ake yi na yakan ta’addanci. Za a dai ci gaba da wannan fafutukar.“

A wata sabuwa kuma, kungiyar kare hakkin dan Adam nan ta Amirka, wato „Human Rights Watch“, ta ce tana sa ido kan duk furace-furacen da Rice ke yi a wannan ziyarar tata a Turai. Wani kakin kungiyar, Tom Malinowski, ya kyautata zaton cewa, jawaban da Rice ke yi a Turai za su dace da matsayin gwamnatin Amirka:-

„Idan dai da gaske gwamnatin Amirkan take, na cewa ta hana duk wasu matakan nuna wa fursunoni azaba, to da babu wata bukata kuma ke nan ta kafa sansanonin sirrin nan da take tsare fursunonin“.

Kawo yanzu dai, ba a sami wani wakilin gwamnatin shugaba Bush da ya karyata cewa, Amirka ba ta da wadannan sansanonin.