1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rene Preval na kan gaba a zaben shugaban kasar Haiti

February 10, 2006
https://p.dw.com/p/Bv8h

Tsohon shugaban kasar Haiti Rene Preval ya doshhi hanyar lashe zaben shugaban kasar na farko tun bayan kifar da gwamnatin Jean-Bertran Aristide shekaru biyu da suka wuce. Ko da yake kawo yanzu hukumar zaben kasar ta Haiti ba ta ba da wani sakamakon zaben na ranar talata ba, amma kuri´un da aka kidaya a wasu tashoshi zabe sun nuna cewa mista Preval na kan gaba da kuri´u masu yawan gaske. ´Ya´yan tawagarsa a zaben da kuma sauran ´yan takaran shugaban kasa sun ce Preval na kan gaba da yawan kuri´u. Preval dai na bukatar sama da kashi 50 cikin 100 na yawan kuri´un da aka kada don kauracewa gudanar da zagaye na biyu na zaben a ranar 19 ga watan maris. A wani lokaci yau da yamma ake sa ran samun sakamakon hukuma na wannan zabe.