1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Regintan masu zabe a Liberia.

Ana samun matsaloli na rashin masu fitowa domin yin registan sunayensu a Liberia,gabannin zaben shugaban kasa dana yan majalisar dokokin kasar

default

MOD.:Alummar kasar Liberia sun shiga yini na biyu na yin registan masu zabe,a karo na farko tun bayan da kasar ta tsira daga rikicin yakin basasa daya dauki shekaru 14 yana gudana.

A ranar 11 ga watan oktoban wannan shekara ne aka tsara gudanar da zaben shugaban kasa dana yan majalisar dokoki a Liberia,wanda ke nuni da dasa aya kann rikicin daya haddasa asaran rayukan kimanin mutane dubu dari biyu da hamsin ,tare da mayar da dubban wasu yan gudun hujira,kana wasu suka tsinci kansu cikin mawuyacin hali na rashin kayayyakin more rayuwa.

Shugaban gwamnatin rikon kwarya wanda kuma ke jagorancin kasar tun daga kawo karshen yakin basasa a shekara ta 2003 Gyude Bryant,ya bayyana takaicinsa dangane da alummar Liberia suka ki fitowa domin regista a wannan yunkuri da aka sanya gaba na samarwa kasar zababbiyar gwamnatin farar hula.

Rahotanni na nuni dacewa cibiyoyi kalilan a birnin Monrovia wanda ke zama fadar kasar,mutane sukayi dafifiv domin yin Registan sunayensu.Akasarin sassan na Monrovia dai sun kasance ba tare da wutan lamtarki ba ballantana ruwan fanfo tsawon shekaru 10 da suka gabata.

Wasu yan kasar na masu raayin cewa ,kamata yayi a wayerwa da jama a kai dangane da muhimmancin wannan shiri dake gudana,tunda batu ne daya shafi kasa baki daya.Tuni wasu dai suka bayyana rashin masaniya dangane da bukatar yin regista gabannin zaben.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Liberia dai na kyautata zaton cewa kimanin alummar kasar million daya da dubu dari biyar ne zasuyi regista a cibiyoyi kimanin 1,da dari biyar da aka tanadar a sassa daban daban na Liberian.

Yantattun bayin Amurka ne suka kafa Liberia sama da shekaru 150 da suka gabata,kuma ta kasance daya daga cikin kasashen dake cikin zaman lafiya a wancan lokaci,kafin ta tsinci kanta cikin rikicin yan tawaye na shekaru masu yawa.

Daga cikin mutane 40 da zasuyi takarar shugabancin Liberia,harda dan uwan tsohon shugaban kasar wanda kuma yafi kowanne jimawa kann karagar mulki ,Winsto Tubman,sanannen dan tsohon dan wasan kwallon nan George Weah da kuma tsohon jamiin Bankin duniya Ellen Johnson-Sirleaf.

Ayayinda ake cigaba dayiwa jamaa regista gabannin zaben na watan Oktoba,masu lura da alamura dakaje suzo sun jaddada bukatar ilimantar tare da wayerwa da jammaa kai dangane da muhimmancin yin regista kafin zabe.

 • Kwanan wata 26.04.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvcI
 • Kwanan wata 26.04.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvcI