Real Madrid ta lashe kofin zakarun Turai | Labarai | DW | 29.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Real Madrid ta lashe kofin zakarun Turai

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta Spain ta lashe kofin gasar kwallon kafa ta zakarun Turai ta wannan shekara a karawar da suka yi da Atletico Madrid itama ta kasar ta Spain a daran jiya Asabar.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta Spain ta lashe kofin gasar kwallon kafa ta zakarun Turai ta wannan shekara a karawar da suka yi da Atletico Madrid itama ta kasar ta Spain a daran jiya Asabar a filin wasa na San Siro na birnin Milan a kasar Italiya.

Christiano Ronaldo ne ya ci kwallon karshe da ta bai wa Real Madrid nasarar lashe kofin a yayin bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da aka kawo karshen mintoci 120 na wasa da karin lokaci ana ci daya da daya.

Wannan dai shi ne karo na 11 da Real de Madrid ke lashe wannan kofi ta zakarun Turai