RDC ta kori mutane 32 da ta ke zargi da kitsa juyin mulki | Labarai | DW | 28.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

RDC ta kori mutane 32 da ta ke zargi da kitsa juyin mulki

Ministan harakokin cikin gida na Jamhuriya Demokradiyar Kongo, ya bayana korar mutanen nan 32, na ƙasashen ƙetare, da a ka kama ranar 23 ga watan da mu ke ciki, bayan an tuhume su, da kitsa maƙarshiyar juyin mulki.

Wannan mutane, da su ka haɗa da Amurikawa 3, da 19 yan Afrika ta kudu, da kuma 10 na tarayya Nigeria, ƙurraru ne, ta fannin aikin soja, inji sanarwar ministan.

A halin da ake ciki, sun shiga hannun kotunan ƙasashen su, na assuli, wanda za su yanke masu, hukunci da ya dace.