1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

230909 Muammar al-Gaddafi Porträt

September 23, 2009

Shugaban Libya Muammar Gaddafi ya yi jawabi a Zauren mashawartar Majalisar Ɗunkin Duniya

https://p.dw.com/p/JnSg
Moammar GadhafiHoto: AP

Yanzu dai tsawon mako guda kenan, tun da ƙasar Libya ta karɓi shugabancin babban taron Majalisar Ɗinkn Duniya. Wannan matsayi zai baiwa shugaba Muammar Gaddafi damar cimma burin sa na kasancewa gwarzo a al'amuran Duniya. Ranar Laraba yayi jawabi gaban taron babbar mashawartar majalisar a New York, gaban shugabannin gwamnatoci da na ƙasashe da dama jawabi, Jawabnin sa ya biyo bayan buɗe taron ne da bisa al'ada, shugaban Amerika yakan yi a duk shekara.

A karon farko tun da ya karɓi madafun iko, shekaru arba'in da suka wuce, shugaban Libya Muammar al-Gaddafi yayi tattaki zuwa Amerika, abin da ko kaɗan ba ma za'a kwatanta yiwuwar sa ba 'yan shekaru kalilan da suka wuce. A da can Gaddafi an rika ɗaukar sa a matsayin mai goyon bayan aiyukan tarzoma ne, amma a yau, ya kasance abokin haɗin gwiwa a fannin cinikin man fetur da ƙasar sa take da arzikin sa, kuma abokin haɗin gwiwa a yaƙi da aiyukan tarzoma a Duniya. Duk da haka, masanin al'amuran Libya ɗan ƙasar Switzerland, Hasni Abidi yace Gaddafi mutum ne dake ci gaba da haddasa muhawara a al'amuran sa na yau da kullum.

UN Vollversammlung in New York eröffnet
Zauren mashawartar MajalisaHoto: AP

Yace Gaddafi mutum ne da ba'a saba samun irin sa ba, ba ma a tsakanin ƙasashen Larabawa ba, amma har a duniya baki ɗaya, musamman saboda mukamin da yake rike dashi, wanda babu mai irin sa a Duniya. Da farko dai shine shugaban juyin juya halin Libya tun daga watan Satumba na shekara ta 1969, ko da shike bisa al'ada, juyin juya hali abun ne dakan ɗauki dan gajeren lokaci kawai.

Bisa manufa, Gaddafi baya rike da wani mukami na ƙasa. Ya ƙi yarda a kira shi da sunan shugaban ƙasa ko shugaban gwamnati, inda yake kallon kansa a matsayin shugaban juyin juya hali ne kawai. Tun yana da shekaru 27 da haihuwa ya shugabanci juyin mulki a Libya ya kuma karbar wa kansa mulkin. Tun daga wannan lokaci ya ɗorawa kansa, ko ake kiran sa da sunaye dabam dabam, misali, Sarkin Sarakuna a Afrika ko Imam na dukkanin musulmi ko kuma jagoran Larabawa.

Muammar Gaddafi yakan ɗauki hankalin ƙasashen yamma ne musamman saboda salon shigar tufafin sa da yanayin mulkin sa da tsarin rayuwar sa. A duk inda ya kai ziyara wata ƙasa, yakan fi ƙaunar zama a tanti ne a harabar mai masaukin sa, tare da sojoji mata da ya tanadar masu tsaron sa.

Har ya zuwa 'yan shekarun baya, ƙasashen na yanma sun ɗauki Gaddafi a matsayin mutum ne dake goyon baya da taimakawa aiyukan tarzoma a Duniya. A lokaci guda, ya sanya kafar wando ɗaya da da ƙasashen na yamma, misali ta hanyar sukan manufofi na jari hujja a duk inda ya sami dama, kamar a lokacin taron ƙasashen ƙungiyar 'yan ba ruwan mu a Algiers a shekara ta 1973.

Yace muna ganin kanmu ne a matsayin masu kare ƙasashe masu tasowa, a gwawarmayar 'yantar da kansu daga al'adar nan ta yan mulkin mallaka, da ta mamaye tunani da zukatan su.

UN USA Libyen Muammar al Gaddafi bei der Volversammlung
Moammar GadhafiHoto: AP / United Nations

Sakamakon goyon bayan da ake zargin Gaddafi yana baiwa aiyukan tarzoma, kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ɗorawa Libya takunkumi a fannoni da dama, abin da ya jefa ƙasar cikin hali na kaɗaitaka da koma bayan tattalin arziki, musamman bayan da Gaddafi ya ki amincewa da alhakin bada izinin sanya bom da ya rushe jirgin saman Pan Am a sararin samaniyar Lockerbie a shekara ta 1996. Daga baya Gaddafi ya ga cewar babu wata mafita, illa ya janye daga duk wani abin da ya shafi aiyukan tarzoma. Masanin harkokin Libya, Hasni Abidi yace:

Gaddafi ya gane cewar haɗari gareshi ba daga cikin gida zai samu ba, amma zai zo ne daga ketare, kuma yana da muhimanci gare shi ya sami goyon baya da amincewar kasashen yamma, wadanda a nasu ɓangaren suka shimfiɗa sharuɗɗa da tilas Gaddafi ɗin ya amince dasu.

Nan da nan kuwa Gaddafi ya canza manufofin sa, ya nuna goyon bayan sa ga Amerika a gwagwarmayar ta kan aiyukan tarzoma, ya dakatar da shirin sa na mallakar makaman nuclear, sa'annan ya biya diyyar miliyoyi ga iyalan wadanda suka mutu a harin na Lockerbie.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Zainab Mohammed