1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Raul ya yi alkawarin cigaba da akidar Fidel Castro

Raul: Zan kare akidar da juyin juya hali

Cikin yanayi na jimami da alhini shugaban Cuba Raul Castro ya yi alkawarin ci gaba da akidar dan uwansa Fidel Castro.

Shugaban kasar Cuba Raul Castro ya sha alwashin ci gaba da akidar gwagwarmayar juyin juya hali na dan uwansa Fidel Castro a wani gagarumin gangami da aka yi na karrama marigayin kafin a binne tokar gawarsa. Dubban jama'a sun hallara dauke da tutoci su na rera wakokin gwagwarmyar juyin juya hali da ke tunato da gudunmawar da marigayi Fidelo Castro ya bayar wajen cigaban kasar. Mutuwar fidel Castro ta haifar da zulumi akan ko wane tafarki kasar za ta dauka bayan rashin mutumin da ya jagoranci kasar kusan shekaru hamsin. Jama'a cikin alhini suna zubar da hawaye sun tunato yadda Castro ya dabbaka bayar da Ilmi kyauta da kuma inganta tsarin lafiya a kasar.