Rataye Taha Ramadan | Labarai | DW | 19.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rataye Taha Ramadan

Majiyar Shariah daga kasar Iraki na nuni dacewa a gobe talata ne zaa rataye tsohon mataimakin shugaban kasar Taha Yassin Ramadan,sakamakon hukuncin kisa da aka yanke masa na cin zarafin biladama.Lauya dake wakiltar tsohon prime minista Tareq Aziz,watau Badia Aref ,wanda shima ke fuskantar sharia saboda cin zarafin jama,ya fadawa kamfanin dillancin labaru na Reuters cewa ,iyalan Mr Ramadan sunyi masa waya inda suka bukashi dayayi kira ga shugaban kasa akan ya tsayar da zartar da wannan hukunci.Wata majiya kuwa ta shaidar dacewa wannan kira da iyalansa sukayi,yazo ne ayayinda ake shirin rataye shi gobe ta asubahi.Allah yasa mu cika da imani.