1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasuwar tsofan sakatarae janar na Majalisar Dinkin Dunia Kurt Waldheim

June 14, 2007
https://p.dw.com/p/BuIr

Yau ne tsofan sakatare jannar na Majalisar Dinkin Dunia,bugu da kari, tsofan shugaban kasar Austriya, Kurt Waldhein ya riga mu gidan gaskiya, bayan ya share shekaru 88 a dunia.

Kurt Waldheim, ya jagorancin Majalisar Dinkin Dunia a tsawan shekaru 8, wato daga shekara ta 1972 zuwa 1981.

Sannan ya shugabanin kasar sa, ta Austriya, daga 1986 zuwa 1992.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Dunia mai ci yanzu, Ban Ki Moon, ya aika wasikar ta´aziya ga hukumomin Austriya, inda ya bayyana jan na minji aikin da Kurt Waldheim yayi, ta fannin haskaka martabar Majalisar, da kuma tabbatar da zaman lahia, da adalci a dunia baki daya.