1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

060809 Rasmussen Afghanistan

Sadissou YahouzaAugust 6, 2009

Saban shugaban Ƙungiyar tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen ya kai ziyara farko a ƙasar Afganistan

https://p.dw.com/p/J4kl
Rasmussen ya ziyarci AfganistanHoto: AP

Kwanaki ƙalilan da fara jagoranci, saban shugaban Ƙungiyar tsaro ta NATO,Anders Fogh Rasmussen, ya kai rangadi a ƙasar Afganistan , inda ya gani da ido halin da ake ciki , tare kuma da bayyana sabuwar husa´ar da zai ɓullo da ita, domin kawo ƙarshen wannan rikici.

A ƙarshen ziyara yayi taron manema labarai da shugaban Afganistan Hamid Karzai.

Ƙasar Afganistan dake fama da rikicin ´yanTaliban tun shekara ta 2001,na matsayin baban aikin dake gaban Rasmussen kamar yada shi dakansa ya bayyana jim kaƙan kamin ya fara jagorancin Ƙungiyar tsaro ta NATO:Rikicin Afganistan shine babban ƙalubalen da zani fuskanta a matsayi na, na shugaban NATO.Ƙungiyar NATO da Afganistan aminnan junane, baki ɗaya zamu gama ƙarfi domin yaƙar maƙiya Afganistan.

nan da makonni biyu za a zaɓen saban shugaban ƙasa a Afganistan, Saidai a daidai wannan lokaci Ƙungiyar Taliban ta matsa ƙaimi wajen kai hare hare.Kusan babu ranar da ´yan taliban basu kai hari wanda kuma ke yin sanadiyar mutuwar mutane masu yawa.

Mace macen bai bar sojojin NATO ba bare fara hulla amma shugaban NATO ya alƙawarata ɗaukar matakan raguwar yawan mutanemn dake mutuwa:Abin takaici ba za iya yaƙi ba ,ba tare da an samu asara rayuka ba.Saidai zan tabbatar maku da cewar, dakarunmu za su iya ƙoƙarinsu domin taƙaita asara rayukan fara hula."

Wannan halin rikicin da ƙasar ke fama da shi kwanaki ƙalinan kamin zaɓe na daga mahimman batutuwa da aka tattana tsakanin Anders Fogh Rasmussen da shugaban ƙasar Afganistan Hamid Karzai.Magabatan biyu, sunyi imanin cewar da ƙarfin soja ba za a taɓa cimma nasara yaƙi ba.Hanyar da ta fi dacewa itace tebrin shawara tsakanin ɓangarorin dabam dabam,masu gaba da juna.saboda haka, Rasmussen yace kada baki yana cewa:A shirye nike in ɗauki matakai masu inganci, don cimma masalaha.

A shirye nike in hau tebrin shawara da wakilan al´ummomin dabam dabam, muddun bukatar hakan ta taso.

Ɗaya daga mahimman sharuɗan wanan tattanawa shine tsagaita wuta, to saidai da garaje abun da kamar wuya.

A cikin waan ziyara saban sakatare Janar na Ƙungiyar tsaro ta NATO ya alƙawartawa al´umar Afganistan cewar, NATO na tare da su ko wuya ko daɗi, tare da burin cimma zaman lafiya mai ɗorewa.

Tun dai shekara ta 2001 Amurika da abokan ƙawacenta suka kifar da mulkin ´yan taliban a ƙasar Afganistan, tare da ɗaurin aniyar kawo ƙarshen wannan ƙungiya, to saidai har ya zuwa wannan lokaci, sojojin ƙawancin na fuskantar mummunar turjiya daga dakarun Taliban.

Mawwalafi:Ilka/ Yahouza

Edita: Aliyu