Rashin zaman lafiya a Somalia na ci gaba da tsananta
May 18, 2006Talla
Mutane a kalla biyar ne suka rugamu gidan gaskiya, wasu kuma da dama suka jikkata a can birnin Magadishu na kasar Somalia.
Hakan kuwa ya biyo bayan wani dauki ba dadi ne da akayi a tsakanin yan yakin sa kai na Islama da kuma madugan yaki na kasar.
Wannan arangama dai tazo ne a dai dai lokacin da daruruwan mutane suka gudanar da wata zanga zangar lumana na bukatar zaman lafiya a kasar.
A yan makonni kadan da suka gabata wannan arangama a tsakanin bangarorin biyu an kiyasta cewa tayi ajalin mutane kusan 150 a kasar.