1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tsaro a Najeriya ya ɗauki saban salo

August 6, 2012

Shugaban ƙabilar Ijaw Chief Edwin Clark ya zargi tsofan shugaban Najeriya Janar Ibrahim Babangida da ɗaurewa ƙungiyar Boko Haram gindi a daidai lokacin da 'yan Ogoni suka yi iƙirarin ɓallewa daga Najeriya.

https://p.dw.com/p/15kl0
Image made available on 19 September of militants from the Movement for the Emancipation of the Niger Delta (MEND) as they patrol the volatile oil rich creeks of the Niger delta in Nigeria 18 September 2008. The Movement for the Emancipation of the Niger Delta claimed in a statement on 19 September 2008 it has attacked a pipeline operated by Shell. MEND declared 'war' on Nigeria's oil industry a week ago. EPA/GEORGE ESIRI +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture alliance / dpa

A wani abin da ke nuna ɗaukan sabon salon da matsalar tsaron Najeriya ke ciki, a karon farko fitaccen shugaban 'yan ƙabilar Ijaw na yankin Niger Delta Chief Edwin Clark, ya fito ƙarara ya ɗorawa tsofan shugaban Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida laifi da cewar ya na da masaniya a kan ƙungiyar Boko Haram, lamarin da ya haifar da maida murtani mai zafi daga Janar ɗin.

A lokutan baya dai, shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi kurarin tonon silili na sunayen mutanen da yace sune ke ɗaukan nauyin ƙungiyar da ke kai hare-hare da bama-bamai a yankin arewacin Najeriya ba tare da yin hakan ba, a yanzu da Chief Edwin Clark ɗan yankin Niger Delta ya yi zargin ga Janar Babangida kalamai ne masu nauyi da ke tada hayaƙi a fagen siyasar Najeriya.

Musayar kalamai a tsakanin shugaban 'yan ƙabilar Ijaw Chief Edwin Clark da tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya Janar Ibarahim Babangida, a kan matsalar tsaron Najeriyar inda ta kaiga Chief Clark zargin Janar Babbangida da hannu a kan batun ƙungiyar da ke kai hare hare a yankin arewacin Najeriyar, zargin da Janar Babangida ya yi watsi da shi, to sai dai wannan na nuna ɗaukan sabon salo a kan wannan matsala da aka daɗe ana laluben hanyar shawo kanta. Abinda ya sanya Dr Yunusa Tanko shugaban jam'iyyar NCP bayyana cewa wannan na nuna muhimmin abu guda a kan batun.

DELTA WARRIOR- An Ijaw militant loyal to Dokubo Asari, protects the jetty at Okorota, near Port Harcourt, Nigeria, Friday June 25, 2004. Asari said that they took up arms to fight for the right of the common people of the oil rich niger delta who are often ignored as also against the re-election of Nigerian President, Olusegun Obasanjo. (AP Photo/George Osodi)
Hoto: AP

‘' Dama kasan an ce ranar wanka ba'a ɓoyon cibi, yanzu waɗannan abubuwa sun fara fitowa, 'yan Najeriya sun samu murya kenan ma'ana shine dama can waɗannan shugabanin yaudaramu suke yi da can suna zama ne su yi ƙusƙus, amma yanzu abin ya fito fili. Arewa ce kudu yanzu gashi sun fito suna zargin juna, a can da bamu san abinda suke ciki ba. Wadannan shugabanin Kaman shi Edwin Clark me ya yiwa al'ummar Niger Delta, shi kansa Janar Babbangida ai shugaban alumma ne, baga yaranmu nan basu da aikin yi ba. Tun da axdewa sun dade suna yi haka amma yanzu ga Allah ya tona masa asiri sun zo suna zargin juna''

Ko da yake ba wannan ne karon farko da mutanen da ake ganin dattawa ne a tarayyar Najeriyar ke fitowa fili suna musayar kalamai da ma hallayar yara ƙanana a bainar jama'a ba, to sai dai kasancewar a wannan karon lamari ne da ya shafi batun rashin tsaro a cikin ƙasar, a dai dai lokacin da ake ci gaba da nuna 'yar yatsa a kan wake da laifi a kan lamarin. To sai dai ga Abdurahman Abu Hamisu na cibiyar nazarin ci gaban ƙasa da ke Abuja ya ce guguwar siyasa ce ke ƙara murtuƙewa ba wai magance matsalar ba.

‘'Abinda Edwin Clark ya faɗa ba wani abu bane da zai ba mutane mamaki , faɗan wanda zai karɓi mulki a 2015 ya riga ya fara, inda ya kamata su yi Magana ba zasu yi ba. Edwin Clark ya yi magana, shin a ina yake ne lokacin da 'yan Boko Haram suka hana tsohon shugaban Najeriya Umaru Musa Ya'Adua aiki? Ya yi magana ne, ai bai yi wani magana ba? Lokacin da 'yan Ijaw suka je Atlas Curve suka sa bom ai bai yi magana ba. To kuma in ba zaka yi magana ba ka yi shiru, to za'a sa maka magana a cikin bakinka, tamkar abinda ya faru kenan ga Babangida''

epa03197097 Security officials gather at the site of a bomb blast at 'This Day' Newspaper office in Abuja, Nigeria, 26 April 2012. Newspaper offices in two Nigerian cities were targeted in coordinated bomb blasts, with several casualties reported, the authorities said. The offices of This Day newspaper in the capital Abuja and Kaduna city were attacked. At least one person was killed and many more were injured, officials said. Rescue workers gave conflicting accounts. Some said a suicide bomber blew up the newspaper's building in Abuja, while others said a bomb was planted at the office. The offices of newspapers Sun and Moment in Kaduna, north-central Nigeria, were also targeted in separate blasts. Four people are feared dead in those blasts and dozens injured, the authorities said. EPA/GEORGE ESIRI
Hoto: picture-alliance/dpa

A dai dai lokacin da ake cikin wannan hali na ƙoƙarin fidda kai daga wanke kai da laifi masharhanta na masu bayyana tsoron illar da irin wannan ke da shi ga makomar Najeriyar, musamman sanin matsayin mutanen da ya kamata su ja gaba a bisu don nemo masalaha.

A ƙasa za ku iysa sauraran rahotanin da wakilanmu suka aiko game da zargin da 'yan Ijaw suka yi wa IBB da kuma yunƙurin ɓallewar 'yan ƙabilar Ogoni daga Najeriya

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita : Saleh Umar Saleh